logo

HAUSA

Xi Jinping ya gabatar da jawabi a yayin taron koli na cika shekaru 30 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da kasashen Asiya ta tsakiya

2022-01-25 20:20:33 cri

Xi Jinping ya gabatar da jawabi a yayin taron koli na cika shekaru 30 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da kasashen Asiya ta tsakiya_fororder_src=http___nimg.ws.126.net__url=http%3A%2F%2Fdingyue.ws.126.net%2F2022%2F0124%2F682c0ef8j00r67yhd002oc000u000irm&thumbnail=650x2147483647&quality=80&type=jpg&refer=http___nimg.ws.126

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci taron koli na cika shekaru 30 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da kasashen Asiya ta tsakiya ta kafar bidiyo a yau Talata a nan birnin Beijing, tare kuma da gabatar da muhimmin jawabi.

A yayin jawabinsa, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, nasarar da aka samu a hadin gwiwar Sin da kasashen Asiya ta Tsakiya 5 na tsawon shekaru 30, ya ta'allaka ne ga mutunta juna, da kyakkyawar makwabtaka, da zama tsintsiya madaurinki guda, da samun moriyar juna da nasara tare.

Baya ga haka, Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin tana son yin amfani da damar da ake samu tare da kasashen tsakiyar Asiya, da yin kokari kafada da kafada, don raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Asiya ta tsakiya.

A nasu bangaren, shugabannin kasashe 5 na tsakiyar Asiya, sun ce, suna sa ran halartar bikin bude gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing a mako mai zuwa, suna kuma cike da imanin cewa, kasar Sin za ta shawo kan matsalolin annobar COVID-19, tare da gudanar da wannan gasar wasannin Olympics cikin nasara, wadda tabbas za ta kawo karin tabbaci da fata ga duniya! (Mai fassara: Bilkisu Xin)