logo

HAUSA

Sin ta bukaci a dauki wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing a matsayin wata dama ta kiyaye zaman lafiya da ci gaban duniya

2022-01-25 20:55:20 CRI

Sin ta bukaci a dauki wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing a matsayin wata dama ta kiyaye zaman lafiya da ci gaban duniya_fororder_1000

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya yi kira ga dukkan kasashen duniya, da su dauki gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta birnin Beijing, a matsayin wata dama ta kawar da bambance-bambance ta hanyar tattaunawa, da maye gurbin yin fito-na-fito da hadin gwiwa, da kara fahimtar juna, da kiyaye zaman lafiya da ci gaban duniya.

A jiya ne, yayin da kwanaki 10 suka rage a fara wasannin Olympics na lokacin sanyi na shekarar 2022 a nan birnin Beijing, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya gabatar da jawabi a rubuce, inda ya yi kira ga dukkan kasashen duniya, da su martaba yarjejeniyar dakatar da yaki lokacin wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing. .

Zhao Lijian, ya bayyana wadannan kalamai ne, yayin da yake amsa tambayoyin da abin ya shafa,. Ya kuma tabbatar da cewa, Sarkin Kambodiya Norodom Sihamoni da shugaban majalisar dokokin Koriya ta Kudu Park Byeong-seug, za su halarci bikin bude gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing.