logo

HAUSA

An yi bita ta uku na liyafar Bikin Bazara na 2022

2022-01-25 20:27:04 cri

An yi bita ta uku na liyafar Bikin Bazara na 2022_fororder_1e0f51c6-a090-4198-b18e-56a156b510f4

Yau Talata, babban rukunin gudan rediyo da talabijin na kasar Sin, ya shirya bita ta uku na liyafar Bikin Bazara na 2022. Shirye-shiryen da aka tsara da kyau sun ba masu kallo mamaki da dariya.

Game da abubuwan da aka tsara da ke cikin shirye-shiryen, bikin na wannan shekara yana kokarin hada yanayi na fasaha da na zaman rayuwa waje guda, da nufin kara kayatar da masu kallo. Baya ga shirye-shiryen da suka mayar da hankali kan ci gaba da gadon al'adun gargajiya, akwai kuma wadanda ke mai da hankali kan batutuwan da suka shafi farfado da karkara, wayewar muhallin halittu, wasannin kankara da dusar kankara da wasannin Olympics na lokacin sanyi da dai sauransu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)