logo

HAUSA

Mutane 6 sun rasu a turmutsutsun filin wasan Kamaru

2022-01-25 10:26:18 CRI

Mutane 6 sun rasu a turmutsutsun filin wasan Kamaru_fororder_0125-Kamaru-Saminu

A kalla mutane 6 ne suka rasu, yayin turmutsutsun da ya auku a filin wasan kwallon kafa na birnin Yaounde, yayin da gungun ’yan kallo suka yi yunkurin kutsawa cikin filin wasan da Kamaru ke karawa da Comoros a daren jiya Litinin.

Da yake karin haske game da aukuwar lamarin, gwamnan yankin tsakiyar kasar Naseri Paul Bea, ya ce baya ga wadannan da suka rasu, akwai kuma karin mutane da dama da suka jikkata, kuma tuni aka garzaya da su asibitin birnin Yaounde.

Emmanuel Njomo, wani wanda ya shaida aukuwar al’amarin, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, sama da mutane 1,000 ne suka yi yunkurin kutsawa cikin filin wasan. Ya ce mutanen sun kasa yin hakuri su shiga filin a mutse, domin kallon wasan da an riga an fara buga shi a lokacin, don haka suka fara turereniya, tare da karya shingen da aka sanya, lamarin da ya sabbasa rasuwa, da jikkata mutane da dama, ciki har da yara kanana da mata. (Saminu Hassan)