logo

HAUSA

Xi ya jaddada kwakkwaran aiwatar da shawarwari, shirye-shirye kan kololuwa da tsakatsakin fitar da iskar carbon

2022-01-25 20:25:53 CRI

Xi ya jaddada kwakkwaran aiwatar da shawarwari, shirye-shirye kan kololuwa da tsakatsakin fitar da iskar carbon_fororder_VCG111354645424

Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis mai mulki a kasar Sin(JKS) Xi Jinping, ya jaddada yin nazari sosai kan halin da kasar ke ciki, da kuma ayyukan da aka tsara na ciyar da aikin kololuwa da madaidaicin fitar da iskar carbon, da yin kokari matuka don aiwatar da shawarwari da shirye-shiryen da kwamitin kolin JKS ya yanke.

Xi ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, yayin da yake jawabi a taron nazari na hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS.