logo

HAUSA

Wakilin MDD ya bukaci majalisar dokokin Libya ta tsara jadawalin zaben kasar

2022-01-24 14:00:59 CRI

Wakilin MDD ya bukaci majalisar dokokin Libya ta tsara jadawalin zaben kasar_fororder_220124-ahmad-Libya

Mai bada shawara ga babban sakataren MDD game da batutuwan kasar Libya (SASG), Stephanie Williams ta yi kira ga mambobin majalisar wakilan kasar Libya su fitar da sabon jadawalin shirya manyan zabukan kasar.

Williams ta yi wannan kiran ne a lokacin ganawa da Aguila Saleh, kakakin majalisar wakilan kasar, a birnin al-Gubba dake gabashin kasar.

Stephanie Williams ta ce, halastaciyyar hanyar da za ta warware rikicin siyasar kasar shi ne ta hanyar amfani da akwatin zabe.

A baya dai Libya ta tsara gudanar da zaben shugaban kasar a ranar 24 ga watan Disambar shekarar 2021. To sai dai kuma, an dage gudanar da zaben har sai abin da hali ya yi sakamakon wasu matsalolin dake shafar tsare-tsare da kuma wasu batutuwan da suka jibinci shari’a, kamar yadda babbar hukumar zaben kasar ta bayyana. (Ahmad)