logo

HAUSA

Filayen jiragen saman kasar Sin sun samu karuwar fasinjoji a bara

2022-01-24 14:31:09 CRI

Filayen jiragen saman kasar Sin sun samu karuwar fasinjoji a bara_fororder_220124-saminu-Airport

Filayen jiragen sama na kasar Sin, sun samu karuwar fasinjoji matafiya dake tashi a cikin su a shekarar 2021 da ta gabata.

A cewar wani rahoto na kamfanin samar da bayanai game da harkokin sufurin sama na VariFlight, cikin shekara guda, an samu tashi da saukar jiragen saman fasinjoji a filayen jiragen saman babban yankin kasar Sin har sau sama da miliyan 3.83, karin da ya kai na kaso 7.21 bisa dari a shekarar ta bara.

Kaza lika rahoton ya ce a shekarar da ta gabata, adadin jirage masu tashi daga filayen sun kai kusan miliyan 3.8, yayin da zirga-zirgar fasinjoji ta karu da kaso 9.56 bisa dari idan an kwatanta da na shekarar 2020.

Bisa bayanan rahoton, filayen jiragen saman kasar 22, masu karbar fasinjoji da yawansu ya kai miliyan 10 ko fiye, sun samu karuwar zirga zirga cikin shekara guda. Cikin su akwai Beijing Daxing, wanda ya samu karuwar tafiye-tafiye a bara, sama da na shekarar 2019.

A daya hannun kuma, filayen jiragen sama 9, dake karbar fasinjoji da yawan su ya kai mutum miliyan 30, su ma sun samu karuwar masu tafiye tafiye. Cikin wannan rukuni akwai Guangzhou Baiyun, wanda ke lardin Guangdong a kudancin kasar, wanda ya zo na daya a yawan tashin jirage a shekarar ta 2021.    (Saminu)