logo

HAUSA

An gudanar da atisaye karo na biyu tare da kwalliya don bikin bude gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing

2022-01-23 16:59:14 cri

An gudanar da atisaye karo na biyu tare da kwalliya don bikin bude gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing_fororder_aa97564317fd4d8db81793ece70b8ac0

A yammacin ranar 22 ga wata, an gudanar da atisaye a karo na biyu tare da kwalliya na bikin bude gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing wanda ya janyo hankulan mutane sosai a filin wasa na kasar Sin na "Shekar Tsuntsu". Sabanin wanda ya gabata, wannan atisayen da aka gudanar da dukkan tsari da kuma dukkan abubuwan da suka shafi bikin, kuma kayatattun wasan wuta sun haska sararin sama da dare a "Shekar Tsuntsu" a wannan dare.

Zhang Yimou, wanda ya taba jagorantar bikin budewa da rufe gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekarar 2008, ya sake daukar nauyi na zama babban darektan bikin budewa da rufe gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing da ajin nakasassu na gasar ta shekarar 2022 ta Beijing.

Ya bayyana cewa, bikin bude gasar ya hada da wasan kwaikwayo da shagulgula, kuma yana kokarin gabatar da wani yanayi na soyayya, kyawawa da dumi-duminsu ga duniya ta hanyar hada ra'ayoyin yin kirkire-kirkire a fannin fasaha, kare muhalli da motsa jiki da kiwon lafiya.

Yiannis Exarchos, babban jami'in zartaswa na kamfanin watsa shirye-shiryen wasannin Olympics (OBS), wanda ke da alhakin watsa shirye-shiryen wasannin Olympics na lokacin sanyi, ya isa birnin Beijing, inda ya kalli atisayen bude bikin. Ya ce, bikin bude gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na shekarar 2022 na birnin Beijing ya sha bamban da na gasar wasannin Olympics na lokacin zafi na shekarar 2008 a nan birnin Beijing, amma shi ma yana da matukar burgewa da ban sha'awa, a cewarsa, "Na yi imani cewa, ba ku da wani dalili na tsallake wannan bikin bude gasar." (Mai fassara: Bilkisu Xin)