logo

HAUSA

Gwamantin Burkina Faso ta musanta kwace ikon kasar bayan musayar wuta a barikin soji

2022-01-23 21:09:53 CRI

Gwamnatin kasar Burkina Faso ta tabbatar a yau Lahadi cewa, an samu musayar wuta a barikin sojojin kasar, sai dai ta karyata rahotannin da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani dake nuna cewa sojoji sun kwace ikon kasar.

Da sanyin safiyar yau Lahadi an ji karar harbe-harben bindigogi a barikin sojoji dake Ouagadougou babban birnin kasar. Sai dai kawo yanzu ba a san musabbabin harbe harben ba.(Ahmad)