logo

HAUSA

Tsarin biyan kudi na PAPSS ya samarwa Sinawa masu zuba jari damarmaki

2022-01-22 16:38:00 CRI

An bayyana tsarin biyan kudi na PAPSS dake karkashin yarjejeniyar yankin ciniki cikin ‘yanci ta Afrika, a matsayin wanda ya samar da damarmaki ga Sinawa ‘yan kasuwa, wajen fadada jarinsu a nahiyar.

John Gatsi, shugaban tsangayar nazarin kasuwanci ta jami’ar Cape Coast ta Ghana ne ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, inda ya ce, yayin da kasashen Afrika suka fara amfani da tsarin, Sinawa za su samu saukin sayar da kayayyakinsu a nahiyar.

Ya ce karkashin yarjejeniyar, nahiyar Afrika na ci gaba da bude kofarta ga bangarori da dama. Haka kuma, yayin da aka samar da tsarin biyan kudi tsakanin kasa da kasa, babu makawa, Sinawa masu zuba jari za su ci gaba da amfana da yankin na cinikayya na nahiyar Afrika.

A ranar 13 ga watan Janairu ne, yarjejeniyar kafa yankin ciniki cikin ‘yanci ta nahiyar Afrika da bankin kula da shige da fice na nahiyar, da sauran wasu abokan hulda, suka kaddamar da tsarin PAPSS, wanda ake sa ran zai bunkasa cinikayya a nahiyar, ta hanyar rage dogaro kan biyan kudi ta hanyar wata takardar kudi. (Fa’iza Mustapha)