logo

HAUSA

Sin na fatan MDD za ta bayar da karin gudummawa a fannin warware matsalolin dake gaban kasashe masu tasowa

2022-01-22 16:34:20 CRI

Sin na fatan MDD za ta bayar da karin gudummawa a fannin warware matsalolin dake gaban kasashe masu tasowa_fororder_hoto

Babban magatakardan MDD Antonio Guterres, ya gabatar da rahoto game da muhimman ayyukan da zai mai da hankali kansu a shekarar 2022. Cikin rahoton da ya gabatar ga babban taron MDD a jiya, Antonio Guterres, ya ce, akwai manyan kalubale biyar dake gaban duniya, wato yaduwar annobar cutar COVID-19, da matsalar tsarin sha’anin kudi na duniya, da matsalar sauyin yanayi, da amfani da sabbin fasahohi ta hanyoyin da ba su dace ba, da kuma rikice-rikice. Ya ce, yadda za a warware wadannan matsaloli biyar, zai yi gagarumin tasiri ga makomar bil Adama. Shi ya sa, ya kamata kasashen duniya su dauki matakai yadda ya kamata domin warware wadannan matsaloli daga tushe.

Haka kuma, a yayin taron, mataimakin zaunannan wakilin kasar Sin dake MDD Geng Shuang ya bayyana cewa, a halin yanzu, annobar COVID-19 tana ci gaba da yaduwa cikin kasashen duniya, ana kuma fuskantar matsalar farfadowar tattalin arziki bayan annoba, kana, bambancin dake tsakanin kasa da kasa a fannin samun ci gaba, yana ci gaba da karuwa, lamarin da ya haddasa illa ga ci gaban duniya baki daya. A don haka, kasar Sin tana fatan MDD za ta ba da karin gudummawa ga kasashe masu tasowa a fannin warware manyan kalubalen dake gabansu. Ya ce ya kamata da farko, a aiwatar da tsarin cude-ni-in-cude-ka yadda ya kamata. Sa’a nan, a kara hadin gwiwa domin yaki da annoba. Na uku kuma, a tsaya tsayin daka wajen neman ci gaba. Na karshe kuma, a dukufa wajen neman farfadowar kasashen duniya ta hanyoyi masu kare muhalli. (Maryam)