logo

HAUSA

A karon farko kasar Sin ta zama kasa mafi shigo da koffi daga Habasha

2022-01-21 11:35:11 CRI

A karon farko kasar Sin ta zama kasa mafi shigo da koffi daga Habasha_fororder_0122-ao3-koffi

Kasar Habasha ta samu kudin shigar da ya kai dala miliyan 578 daga cinikin koffi da ta fitar zuwa ketare a cikin watanni shida da suka gabata, lamarin da ya nuna cewa a karon farko kasar Sin ta kasance a matsayin kasa mafi shigo da koffi daga kasar Habasha. Hukumar gudanarwar koffi da ganyen shayi ta kasar Habasha ta sanar da hakan a ranar 20 ga watan Janairu.

A shekarun baya bayan nan, koffin kasar Habasha yana samun karin karbuwa daga masaya Sinawa. A ranar 19 ga watan Janairu, jakadan kasar Habasha a kasar Sin, Teshome Toga Chanaka ya ziyarci dandalin kasuwanci na zamani da aka watsa kai tsaye a kasar Sin, kuma an yi cinikin fakiti 10,000 na koffi din kasar Habasha a cikin dakika biyar, lamarin da ya kara bunkasa huldar cinikayyar kayan amfanin gona a tsakanin Sin da Habasha. (Ahmad)