logo

HAUSA

Jarin kai tsaye da kasar Sin ta zuba a shekarar 2021 ya kai yuan biliyan 930

2022-01-21 11:53:48 CRI

Jarin kai tsaye da kasar Sin ta zuba a shekarar 2021 ya kai yuan biliyan 930_fororder_220121-Ibrahim3-China

Ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin ta sanar a Alhamis, cewa, jarin da kasar ta zuba kai tsaye a ketare, ya samu bunkasuwa mai inganci a bara, inda ya karu da kaso 2.2 bisa dari a shekarar zuwa Yuan biliyan 936.69.

Mai magana da yawun ma’aikatar Shu Jueting, ya bayyana cewa, a bangaren dalar Amurka, jarin kai tsaye na kasar ta zuba a wannan lokacin, ya karu da kashi 9.2 bisa dari a shekara guda da ta wuce, zuwa dala biliyan 145.19.

Alkaluma sun nuna cewa, jarin da bai shafi harkokin kudi ba da kasar ta zuba a cikin kasashen da suka ratsa shawarar ziri daya da hanya daya, ya karu da kashi 14.1 bisa dari a shekara zuwa dalar Amurka biliyan 20.3.

Ma'aikatar ta ce, a shekarar 2021, kasar Sin ta sanya hannu kan sabbin ayyuka 560 da darajarsu ta kai sama da dalar Amurka miliyan 100, fiye da na shekarar da ta gabata. Kuma ayyukan sun fi karkata ne kan bangaren samar da ababen more rayuwa, kamar sufuri.

A cewar bayanan ma’aikatar, ya zuwa karshen shekarar 2021, darajar jarin da kasar ta zuba a yankunan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya na ketare, ta kai dalar Amurka biliyan 50.7, wanda ya ba da gudummawar dalar Amurka biliyan 6.6 na haraji da kudade ga wuraren da aka zuba jari, da samar da ayyukan yi 392,000 a cikin gida.  (Ibrahim Yaya)