logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun lalata haramtattun matatun mai 39 a yanki mai arzikin mai cikin makonni biyu

2022-01-21 10:44:43 CRI

Sojojin Najeriya sun lalata haramtattun matatun mai 39 a yanki mai arzikin mai cikin makonni biyu_fororder_0121-a01-Nigerian troops destroy 39 illegal refineries in oil

Kakakin rundunar sojojin Najeriya ya bayyana cewa, rundunar sojojin a yankin kudancin kasar mai arzikin mai sun yi nasarar lalata haramtattun matatun mai 39 a yankin da suke da masu yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa da sauran bata gari.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja game da ayyukan da sojojin ke gudanarwa a fadin kasar, Benard Onyeuko, kakakin rundunar sojojin Najeriyar ya ce, sojojin rundunar musamman ta Operation Delta Safe sun yi nasarar lalata haramtattun matatun man, wadanda aka gano su a jihohin kudancin kasar da suka hada da Rivers, Abia, Bayelsa, Akwa Ibom da Delta.

Bugu da kari, ya bayyanawa ’yan jaridun cewa, a cikin makonni biyun da suka gabata, sojojin sun yi nasarar lalata haramtattun matatun mai 39, da wuraren dafa abinci 91, da tankokin adana ruwa 24, da manyan rumbuna na karkashin kasa 17, da kuma tankokin ajiya 96.

A cewar jami’in, a samamen da sojojin suka gudanar, sun gano taceccen mai litar 637,500 da man gas na injina lita 950,000 wadanda aka sata daga albarkatun danyen man kasar. (Ahmad Fagam)