logo

HAUSA

Kafofin yada labarai na Afirka ta Kudu na nuna goyon bayansu ga wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing

2022-01-20 10:34:25 CRI

Kafofin yada labarai na Afirka ta Kudu na nuna goyon bayansu ga wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing_fororder_220120-I2-SA

Kwanan nan, manyan kafofin watsa labaru na Afirka ta Kudu irin su Beituo News, da Mercury, da Cape Times da kuma kafofin watsa labaran yanar gizo masu zaman kansu, sun wallafa sharhi mai taken "Gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, tana nuna ruhin bil-adama maras iyaka". Suna masu cewa, gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, ta kunshi mutane daga ko'ina a duniya. Suna kuma da kyakkyawan fatan cewa, gasar za ta tabbatar da mafarkin da daukacin bil- Adam ke da shi.

Kamar yadda aka ambata a cikin sharhin, a matsayinta na kasa mai son zaman lafiya da harkokin wasanni, kasar Afirka ta Kudu tana ba da cikakken goyon baya tare da sanya ido kan wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing dake tafe.

Sharhin ya yi imanin cewa, a cikin wannan mawuyacin lokaci da annobar COVID-19 ke ci gaba da yaduwa, gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi, ba kawai za ta iya kawar da matsin lamba na wani dan lokaci ba, har ma za ta kara kwarin gwiwar jama'a da taimakawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya. A daidai lokacin da duniya ke ci gaba da fama da kalubale irin su annobar COVID-19, da matsalar sauyin yanayi, hadin kai da abota tsakanin kasashe, su ne mafi muhimmanci. (Ibrahim Yaya)