logo

HAUSA

WHO: An samu raguwar masu harbuwa da COVID-19 a Afirka bayan sake bullar cutar a karo na 4

2022-01-20 20:23:13 CRI

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta sanar da raguwar adadin masu harbuwa, da masu rasuwa sakamakon cutar COVID-19 a sassan nahiyar Afirka, bayan bullar cutar a zagaye na 4.

Sabon rahoton da ofishin shiyyar Afirka na WHOn ya fitar a Alhamis din nan, ya nuna cewa, ya zuwa karshen makon jiya, adadin masu harbuwa daga cutar ya ragu da kaso 20 bisa dari, yayin da na masu rasuwa sakamakon ta ya ragu da kaso 8 bisa dari.   (Saminu)