logo

HAUSA

Wani turmutsutsu ya sabbaba rasuwar a kalla mutane 30 a Liberia

2022-01-20 19:17:38 CRI

Rahotanni daga wasu kafofin kasar Liberia na cewa, a jiya Laraba, wasu gungun masu zanga zanga sun rika sukan mutane da wukake, yayin wani taron addini da ya gudana a garin New Crewe, wanda ke arewa maso yammacin birnin Monrovia, fadar mulkin kasar.

Rahotannin su ce, mutane sun rika kokarin tserewa daga taron sakamakon harin masu zanga zangar, wanda hakan ya haifar da turmutsutsu, aka kuma rika tattake wasu mutanen, lamarin da ya kai ga rasuwar a kalla mutane 30, ciki har da kananan yara 11.  (Saminu)