logo

HAUSA

Yawan jarin wajen kai tsaye na Sin ya kai yuan biliyan 936.69 a 2021

2022-01-20 16:42:13 CRI

Yawan jarin wajen kai tsaye na Sin ya kai yuan biliyan 936.69 a 2021_fororder_jari

A ranar Alhamis 20 ga watan Janairu, ma’aikatar ciniki ta kasar Sin ta bayyana cewa, jarin waje da hadin gwiwar bunkasa ci gaba na kasar Sin ya karu a shekarar 2021, inda adadin jarin waje na kai tsaye na kasar ya kai kudin Sin yuan biliyan 936.69, kwatankwacin dala biliyan 147.85 a dukkan sana’o’i, inda ya karu da kashi 2.2 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokaci na shekarar 2020.

A cewar Zeng Yande, masanin kimiyyar noman tsirrai, kana daraktan sashen tsara dabarun ci gaba na ma’aikatar aikin gona da raya karkara ta kasar Sin ya bayyana cewa, adadin kudaden shigar mazauna karkara a kasar Sin ya kai yuan 18,931 kwatankwacin dala 2,984 a shekarar 2021, inda aka samu karin kashi 9.7 bisa 100, wanda ya karu da kashi 2.6 sama da adadin na mazauna biranen kasar.(Ahmad)