logo

HAUSA

Sinawa na sahun gaba wajen amincewa da gwamnatinsu a shekarar 2021

2022-01-20 19:11:44 CRI

Sinawa na sahun gaba wajen amincewa da gwamnatinsu a shekarar 2021_fororder_jks

Wasu rahotanni sun nuna cewa, tsakanin al’ummun kasashen duniya daban daban, Sinawa na sahun gaba a fannin amincewa da gwamnatinsu, inda wasu alkaluma suka nuna yawan Sinawa da suka tabbatar da amincewa da gwamnatin kasar Sin ya kai kaso 91 bisa dari a shekarar 2021 da ta gabata.

Da yake tsokaci game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce hakan ba abun mamaki ba ne, duba da yadda JKS da gwamnatin Sin ke aiki tukuru wajen cimma muradun al’ummar kasar.

Zhao Lijian ya kuma ce a jiya Laraba, Sin ta gabatar da tallafin jin kai na gaggawa ga tsibirin Tonga, kuma za ta ci gaba da mika kudade da kayayyakin bukata domin tallafawa tsibirin gwargwadon bukata, biyowa bayan ibtila’in aman wuta na dutse da ya auku a kasar.  (Saminu)