logo

HAUSA

Shugabannin kasashen Sin da Belarus sun taya juna murnar cika shekaru 30 da kulla huldar jakadanci

2022-01-20 13:57:56 CRI

Shugabannin kasashen Sin da Belarus sun taya juna murnar cika shekaru 30 da kulla huldar jakadanci_fororder_220120-I3-Xi

Yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Belarus Alexander Lukashenko, suka yi musayar sakon taya juna murnar cika shekaru 30 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Belarus.

Xi ya kara da cewa, bangarorin biyu sun gina amincewa da juna ta fuskar siyasa, da ba za ta taba gushewa ba, sun kuma aiwatar da hadin gwiwa mai inganci a fannoni daban-daban. Shugaba Xi ya kara da cewa, suna ci gaba da nuna goyon baya ga juna kan batutuwan da suka shafi babbar moriyarsu, da yin hadin gwiwa yadda ya kamata a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya.

A nasa bangare, shugaba Lukashenko ya bayyana cewa, a cikin shekaru 30 da suka gabata, an daga matsayin dangantakar kasashen Belarus da Sin daga dangantakar abokantaka ta sada zumunta, zuwa kyakkyawar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, da yin hadin gwiwa da samun nasara tare, da samar da sakamako mai kyau a fannoni daban daban.

Ya ce, yana da kwarin gwiwar cewa, al'ummar kasashen biyu za su ci gaba da ganin dorewar kyakkyawar abota da taimakon juna daga zuriya zuwa zuriya. (Ibrahim Yaya)