logo

HAUSA

Zakarar wasannin Olympic ta Birtaniya Deas za ta jagoranci tawagar ’yan wasan kasar a wasannin Olympics na Beijing

2022-01-20 11:09:07 CRI

Laura Deas, wacce ta lashe lambobin yabo na Olympics za ta jagoranci tawagogin wasannin Olympics uku domin wakiltar kasar Birtaniya a gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing 2022.

Kungiyar wasannin Olympic ta Birtaniya (BOA) ta sanar da cewa, cikin wadanda za su wakilci kasar Birtaniya a gasar an zabi fitattun ’yan wasa hudu da suka hada da Deas, Brogan Crowley, Matt Weston, Marcus Wyatt domin fafatawa a gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Beijing 2022. (Ahmad Fagam)