logo

HAUSA

BRICS za su kara samar da dabarunsu ga daidaita kalubale na bai daya da dan Adam ke fuskanta

2022-01-20 10:57:41 CRI

BRICS za su kara samar da dabarunsu ga daidaita kalubale na bai daya da dan Adam ke fuskanta_fororder_b812c8fcc3cec3fdf695204a981c153686942787

A jiya ne aka rufe taron masu gudanar da harkokin kasashen BRICS karo na farko a shekarar 2022 da muke ciki, kuma a yayin da Mr. Ma Zhaoxu, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin, kana jami’in kula da harkokin kasashen BRICS na kasar Sin yake zantawa da manema labarai, ya bayyana cewa,“Taron ya kasance na farko, tun bayan da kasar Sin ta karbi shugabancin kungiyar, inda ake bikin kaddamar da ‘shekarar kasar Sin’ na kungiyar a hukumance. Yanzu haka gamayyar kasa da kasa na fatan ganin kasashen BRICS za su kara taka muhimmiyar rawa, wajen inganta ayyukan kandagarkin cutar Covid-19 da farfado da tattalin arziki da ma kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.  Sin a matsayinta na kasar da ke shugabantar kungiyar, za ta yi iyakacin kokarin gudanar da taron ganawar shugabannin kasashen kungiyar a wannan shekara, tare da samar da karfin kasar Sin na inganta hadin kan kasashen, da samar da karin dabaru ga kungiyar wajen daidaita kalubale na bai daya da dan Adam ke fuskanta.”

BRICS za su kara samar da dabarunsu ga daidaita kalubale na bai daya da dan Adam ke fuskanta_fororder_d62a6059252dd42a05cc204853af9abccbeab8ad

Baya ga haka, kasar Sin za ta nace ga bin alkiblar tabbatar da ci gaba tare da hada hannu da sauran mambobin kungiyar, ta yadda za su mai da hankali wajen kiyaye moriyar kasashen masu tasowa, da hada karfi da karfe, don gaggauta aiwatar da shirin samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030, don samar da alheri ga jama’ar kasashe biyar na kungiyar da ma na duniya baki daya. (Lubabatu)