logo

HAUSA

Mataimakin ministan harkokin wajen Sin: Samar da ci gaba ne jigon taken shekarar kasar Sin ta kungiyar BRICS

2022-01-19 20:32:02 CRI

A yau Laraba, mataimakin ministan harkokin wajen Sin, kuma babban jami’in tsare tsare na kasar Sin a kungiyar BRICKS Ma Zhaoxu, ya bayyana samar da ci gaba, a matsayin jigon taken shekarar kasar Sin a kungiyar BRICS.

Ma Zhaoxu, wanda ya bayyana hakan, yayin wata zantawa game da matsayin shugabancin karba karba na kungiyar BRICKS da Sin ke rike da shi a bana, ya ce samar da ci gaban hadin gwiwa mai nagarta, da kirkirar sabon yanayin ci gaban duniya, su ne farko da karshen duk wani ci gaba da duniya ke fatan samu.

Ma ya kuma bayyana fatan ganin hadin gwiwar kasashe mambobin kungiyar BRICS, ya haifar da babban ci gaba a wannan shekara ta bana.  (Saminu)