logo

HAUSA

Kudin shigar manyan kamfanonin gwamnatin tsakiyar Sin ya kai yuan triliyanCRI 36.3 a bara

2022-01-19 15:56:36 CRI

Kudin shigar manyan kamfanonin gwamnatin tsakiyar Sin ya kai yuan triliyanCRI 36.3 a bara_fororder_peng huagang

A yau ne, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya gudanar da taron manema labarai, inda babban sakataren hukumar kula da kadarori ta majalisar gudanarwar kasar Sin Peng Huagang, ya bayyana a gun taron cewa, ci gaban da manyan kamfanoni karkashin gwamnatin tsakiya ta kasar suka samu, ya nuna yadda suka goyi bayan kara matakan inganta jimillar tattalin arzikin kasar da GDP na kowane mutum.

A shekarar 2021, manyan kamfanoni na gwamnatin tsakiya sun samu kudin shiga na aiki da ya kai yuan triliyan 36.3, wanda ya karu da kashi 19.5 cikin dari a duk shekara da kuma karuwar shekaru biyu da kaso 8.2%.(Ibrahim)