logo

HAUSA

Zhao Lijian: karfafa kwarin gwiwa da taimakawa juna ne kadai za su iya ingiza nasarar yaki da annoba

2022-01-19 19:08:16 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce karfafa kwarin gwiwa, da taimakawa juna ne kadai za su iya ingiza nasarar yaki da annobar COVID-19 a tsakanin sassan duniya.

Zhao ya bayyana hakan ne a Larabar nan, yayin taron manema labarai da ya gudana, inda kuma ya yi tsokaci game da rahoton hukumar kare hakkin bil adama mai taken “Masu ba da kariya”, rahoton a cewar jami’in na Sin, ya baiwa masu aikata cin hanci da suka tsere daga Sin kariya, ya kuma wanke ayyuka masu nasaba da rashawa.

Zhao ya kara da cewa, Sin ta yi matukar kaduwa, tare da watsi da kalaman jagororin kasar Slovenia, bisa matakin su na goyon bayan samun ‘yancin kan yankin Taiwan, matakin da ya yi matukar keta ka’idar nan ta kasar Sin daya tak a duniya. (Saminu)