logo

HAUSA

Kasar Sin ta bayyana jerin manyan ci gaban kimiyyar da aka samu a duniya a shekarar 2021

2022-01-19 11:09:17 CRI

Kasar Sin ta bayyana jerin manyan ci gaban kimiyyar da aka samu a duniya a shekarar 2021_fororder_220119-yaya3-kimiyya

Jiya ne kasar Sin ta gabatar da jerin sunayen manyan ci gaban kimiyya 10 da kasar ta samu a shekarar 2021 da ma duniya baki daya, kamar yadda mambobin kwalejin kimiyya ta kasar Sin (CAS) da mambobin kwalejin nazarin aikin injiniya ta kasar (CAE) suka zaba.

Masana ilimin kimiyya daga kwalejojin biyu wato CAS da CAE sun rike mukaman ilimi mafi girma a fannin kimiyya da injiniya na kasar Sin.

Daga cikin ci gaban kimiyya da aka lissafa, ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin aikin binciken hasken rana na farko, shi ne ya fi yin fice.

Hukumar kula da binciken sararin samaniyar kasar Sin ta fitar da wasu sabbin hotuna, da na’urar binciken duniyar Mars na farko na kasar wato Zhurong ta dauka, wadanda suka hada da filin da na’urar ta sauka, da yanayin duniyar Mars, da hoton da na’urar ta dauki kanta, wanda ke nuna cikakken nasarar aikin binciken duniyar Mars na farko da kasar Sin ta samu.

Na gaba a jerin manyan ci gaban kimiyya 10 a duniya, shi ne kera na'ura mai sarrafa kanta ta farko, da kokarin kara kera wasu a nan gaba.

Zabar manyan ci gaban kimiya 10 a kasar Sin da ma duniya baki daya, da kwalejojin CAS da CAE suka shirya a lokuta 28, suna taka muhimmiyar rawa wajen yada sabbin ci gaban fasahar kimiyya a cikin gida da kuma waje. (Ibrahim)