logo

HAUSA

Jami’in MDD a Sin ya jinjinawa hadin gwiwar Sin da Afirka

2022-01-19 20:08:40 CRI

Jami’in MDD a Sin ya jinjinawa hadin gwiwar Sin da Afirka_fororder_mdd

A jiya Talata ne, babban jami’in tsare tsare na ofishin MDD dake kasar Sin Siddharth Chatterjee, ya bayyana gamsuwa da irin kyakkyawan yanayi da hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ke ciki, yana mai bayyana hakan, a matsayin muhimmin mataki na ingiza wanzuwar ci gaban duniya.

Jami’in ya bayyana hakan ne a nan birnin Beijing, yayin da yake halartar wani taron karawa juna sani, mai nasaba da nazarin sakamakon taro na 8 na ministocin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC.

Mr. Chatterjee ya kara da cewa, Sin na matsayi na biyu a duniya ta fuskar karfin tattalin arziki, yayin da nahiyar Afirka ke da mokama mai haske a fannonin ilimin likitanci, da bunkasar tattalin arziki maras gurbata muhalli, da ma sauran wasu fannoni, yayin da a daya hannun, MDD ke ci gaba da mara baya ga Sin da Afirka, ta yadda za su amfani da albarkatu, da hade bangarorin da suke da fifiko waje guda. Kaza lika majalissar a shirye take, ta zamo mai zaburar da duk wani yanayi na bunkasa hadin gwiwar sassan biyu.  (Saminu)