logo

HAUSA

Wakilin kasar Sin a MDD ya yi kira a kara kare mata a yankunan dake fama da rikici

2022-01-19 11:16:39 CRI

Wakilin kasar Sin a MDD ya yi kira a kara kare mata a yankunan dake fama da rikici_fororder_Img329805046

Zaunannen wakilin kasar Sin dake Majalisar Dinkin Duniya, Mista Zhang Jun ya yi jawabi a yayin zaman muhawarar kwamitin tsaron majalisar kan batutuwan mata da zaman lafiya da tsaro, inda ya yi kira a kare muradun mata daga dukkanin fannoni a yankunan dake fama da rikici.

Zhang ya ce, kare matan dake fuskantar matsalar rikici, da taimaka musu shiga ayyukan warware matsaloli a siyasance a wuraren dake fama da rikici, muhimmin abu ne cikin jadawalin aikin kwamitin sulhun a fannonin da suka shafi mata da zaman lafiya da tsaro.

Zhang ya kara da cewa, a matsayinta na kasar da ta karbi bakuncin babban taron matan duniya karo na hudu, Sin ta jima da bada shawara gami da kira da a tabbatar da daidaiton jinsi da kare muradun mata, da taimakawa ci gaban harkokin mata a duniya. Kana, tana daukar matakan zahiri don aiwatar da jadawalin aiki a fannonin mata da zaman lafiya da tsaro. Malam bahaushe kan ce, kallabi tsakanin rawuna. Kasar Sin na fatan hada kai da sauran kasashen duniya, don baiwa mata dama da taimakawa ci gabansu, da mara musu baya wajen kara taka rawa a harkokin zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa, don raya duniya mai kyakkyawar makoma. (Murtala Zhang)