logo

HAUSA

Sin ta yi kira a inganta hadin-gwiwa tsakaninta da kungiyar G77

2022-01-19 11:33:48 CRI

Sin ta yi kira a inganta hadin-gwiwa tsakaninta da kungiyar G77_fororder_W020210912397327908954

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake Majalisar Dinkin Duniya, Dai Bing, ya gabatar da jawabi a wajen taron jakadu na kungiyar G77 da kasar Sin, inda ya yi kira da a karfafa hadin-gwiwa don yin magana da murya daya a dandalin majalisar.

Jakada Dai ya ce, a halin yanzu duniya na fuskantar manyan sauye-sauye, kana, matsalar nuna bangaranci da ra’ayin bada kariya ga harkokin kasuwanci na dada tsananta, yayin da tattalin arzikin duniya bai farfado yadda ya kamata ba, kuma annobar COVID-19 ke ci gaba da yaduwa, al’amuran da suka sa kasashen duniya kokarin lalubo hanyoyin magance su. A matsayinta na tsarin hadin-gwiwar kasashe masu tasowa mafi girma, kungiyar G77 na da nauyi na musamman wajen kiyaye muradun kasashe masu tasowa a sabon zamanin da muke ciki. Don haka, ya dace a karfafa hadin-gwiwa, da yin kira da a kara bude kofa da samun moriya tare, don yin magana da murya daya a dandalin MDD, da shaida karfin adalci da daidaito. (Murtala Zhang)