logo

HAUSA

Menene samar da ci gaba da wadata tare?

2022-01-19 15:57:56 CRI

Menene samar da ci gaba da wadata tare?_fororder_图片1

Samar da ci gaba ga kasashe daban-daban shi ne ainihin ci gaba, samun wadata ga kowa da kowa shi ake nufi da wadata na ainihi.

A ranar 17 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na bana ta kafar bidiyo daga nan Beijing, inda ya shaidawa duniya abin da ake nufi da “wadatar kasar Sin baki daya”. Shugaba Xi ya ce, samar da ci gaba da wadata tare, ba yana nufin kowa yana samun kudi daidai da kowa ba, ya dace a kara samun kudin shiga gaba daya, sa’annan a raba su bisa tsarin da ya dace, ta yadda nasarorin ci gaba za su kara amfanar da daukacin jama’a bisa tsari na adalci. (Murtala Zhang)