logo

HAUSA

Zhao Lijian ya yi tsokaci game da jawabin shugaba Xi a taron WEF na bana

2022-01-18 19:15:37 CRI

A Talatar nan ne, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya yiwa manema labarai fashin baki game da jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, a taron tattalin arziki na duniya na bana.

Zhao Lijian ya ce, annobar COVID-19 ta wanzu har tsawon shekaru 3, kuma farfadowar tattalin arzikin duniya ya gamu da rashin tabbas. A kuma wannan gaba ne shugaba Xi Jinping, ya sake gabatar da jawabi a taron WEF, inda ya bayyana shawara ga sassan kasa da kasa, ta hada kai da juna domin shawo kan cutar, wanda hakan zai zamo ginshiki na musamman, na ingiza farfadowar tattalin arzikin duniya bisa daidaito, kuma hakan zai zamo hanya ta zahiri wadda za ta cike gibin ci gaba, da ma kyautata alakar da ake da ita yanzu tsakanin kasashe daban daban.

Ya ce shugaba Xi, ya karfafa gwiwar dukkanin sassa, game da yiwuwar aiwatar da matakan yaki da annobar COVID-19, da farfado da tattalin arzikin duniya.     (Saminu)