logo

HAUSA

Zhao Lijian: Sin za ta gabatar da tallafin gaggawa ga tsibirin Tonga

2022-01-18 19:40:05 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce Sin za ta gabatar da tallafin kayan jin kai ga tsibirin Tonga, wanda ya sha fama da bala’in dutse mai aman wuta, bisa bukatar mahukuntan tsibirin dake kudancin tekun Fasifik.

Zhao Lijian, wanda ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai na Talatar nan, ya kuma soki lamirin wani tsarin aiki kan kasar Sin, da ma’aikatar shari’ar Amurka ta shelanta. Ya ce kasar Sin na fatan Amurka za ta gaggauta gyara kuskuren ta, tare da dakatar da daukar Sin a matsayin wata boyayyiyar abokiyar gaba.  (Saminu)