logo

HAUSA

South China Morning Post: Me ya sa kasar Sin ta cancanci karbar bakuncin gasar Olympics ta lokacin sanyi ta 2022

2022-01-18 14:49:27 CRI

South China Morning Post: Me ya sa kasar Sin ta cancanci karbar bakuncin gasar Olympics ta lokacin sanyi ta 2022_fororder_220118-i02-Why China deserves to host the 2022 Winter Olympics

Nan da 'yan makonni kadan ne, birnin Beijing na kasar Sin zai karbi bakuncin gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi karo na 24, abin da ya sa babban birnin kasar ta Sin, zama birni na farko a duniya da ya karbi bakuncin gasar wasannin Olympics na zafi da na lokacin sanyi.

Shin me ya sa kasar Sin ta cancanci karbar bakuncin gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta 2022? Da farko, kasar Sin ta samu nasara, ga kyawawan kayayyakin more rayuwa, da wuraren wasanni da ake da su, ga kuma tallafin kudi daga gwamnati. Kauracewa wasannin motsa jiki ba zai kai ga cimma manufofin siyasa ba, illa cutar da 'yan wasa ne kawai. Bincike ya nuna cewa, gasar wasannin Olympics ta shekarar 2008, ta yi tasiri matuka ga al'ummar kasar Sin, da tattalin arziki da muhalli, kuma karbar bakuncin gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi da zai gudana a birnin Beijing, zai ci gaba da fadada matsayin wasanni a kasar.  (Ibrahim Yaya)