Koriya ta arewa ta harba makami mai linzami tekun gabashin Koriya ta kudu
2022-01-17 14:50:55 CRI
Babban jami’in tawagar dakarun tsaron hadin gwiwa na Koriya ta kudu JCS, ya bayyana a yau Litinin cewa, Koriya ta arewa DPRK ta harba makami mai linzami da ba a tantance nau’insa ba zuwa tekun gabashin Koriya ta kudu, koda yake ba a yi cikakken bayani kan lamarin ba.
Wannan shi ne karo na hudu da DPRK ta harba makamai masu linzami a wannan shekarar.
Kamfanin dillancin labaran DPRK ya bayyana a makon jiya cewa, Koriya ta arewan ta yi nasarar gwaje-gwajen makamai masu linzamin biyu a ranar Juma’a.
Koriya ta arewan ta ce ta yi nasarar gwajin makamai masu linzami masu matsanancin gudu a ranar 5 da kuma 11 ga watan Janairu. (Ahmad)