logo

HAUSA

Sin a shirye take ta taimakawa Tonga idan an bukaci hakan

2022-01-17 10:45:34 CRI

Sin a shirye take ta taimakawa Tonga idan an bukaci hakan_fororder_220117-Ahmad 1-Tonga

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, kasar ta lura da halin da ake ciki na iftila’in aman wutar dutse gami da bala’in ambaliyar teku da tartsatsin tokar aman wutar dutsen da aka samu a tsibirin Tonga, kuma a shirye take ta tallafa idan yankin Tongan ya bukaci hakan.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin ya bayyana cewa, ofishin jakadancin kasar Sin dake Tonga ya kammala dukkan tanadin dauki gaggawa, kuma ya lura da yanayin da Sinawa mazauna yankin ke ciki bayan faruwar bala’in ta hanyoyi daban daban. Kawo yanzu, ba a samu wani rahoton hasarar rayukan Sinawa mazauna yankin ba.

Ya bayyana cewa, Sin da Tonga muhimman abokan hadin gwiwa ne. Wang ya ce, kasar Sin ta gabatar da sakon jajantawa gwamnati da al’ummar tsibirin Tonga, kuma a shirye take ta bayar da dukkan taimako da tallafin da ya dace bisa bukatar da Tonga ya nema. (Ahmad)