logo

HAUSA

Sinawa da dalibai dake kasashen waje sun karyata jita-jita kan Xinjiang

2022-01-17 11:50:43 CRI

Sinawa da dalibai dake kasashen waje sun karyata jita-jita kan Xinjiang_fororder_220117-yaya 2-Xinjiang

Sinawa da daliban jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, sun yi tir da jita-jita da batanci da makiya kasar Sin a Amurka da kasashen yammacin duniya suka kitsa, a yayin wani taron musayar ra’ayi ta kafar bidiyo da suka shirya a birnin Urunqi.

Kamran Ekramjan, wani dalibi dan kasar Sin dake jami'ar Anadolu dake kasar Turkiyya ya ce, “mutane su kan tambaye ni game da jihar Xinjiang, kuma a ko da yaushe ina nuna musu hotunan garinmu, duk sun yi mamakin ci gaban da jihar Xinjiang ta samu. Don haka, ina adawa da duk wani batanci da ake yiwa jihar Xinjiang."

Kamiljan Ruza na kungiyar matasan ’yan kasuwar Turkiyya da Sin, ya shiga harkokin kasuwancin kasashen waje a Turkiyya tsawon shekaru.

A shekarar da ta gabata, shi da sauran mambobin kungiyar, suka shirya baje kolin hotuna, don nuna nasarorin da kasar Sin ta samu a shekarun baya. Maziyarta baje kolin sun yaba da ci gaban da kasar Sin ta samu. (Ibrahim)