logo

HAUSA

Xi ya jaddada muhimmancin samar da ci gaban bai daya da hadin gwiwar cimma moriyar juna

2022-01-17 20:20:33 CRI

Xi ya jaddada muhimmancin samar da ci gaban bai daya da hadin gwiwar cimma moriyar juna_fororder_xi

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce kasashe daban daban na da damar samun ci gaba tare, idan sun martaba junan su, sun kuma nemi hanyar samun moriya daga juna, ta hanyar jingine banbance banbance.

Shugaba Xi ya bayyana hakan ne, yayin da yake jawabi ga mahalarta taron tattalin arziki na kasa da kasa da ya gudana a Litinin din nan ta kafar bidiyo. Ya ce hanya mafi dacewa da bunkasa rayuwar dan Adam ita ce, samar da ci gaba cikin lumana da hadin gwiwar cimma moriyar juna.

Shugaba Xi, ya kuma yi kira ga sassan kasa da kasa da su lura da yanayin abubuwan da suka wakana a tarihi, su yi aiki domin samar da daidaito ga dokokin kasa da kasa, su yayata ka’idojin ciyar da bil adama gaba, tare da gini al’umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil adama.

Ya kuma bukaci kasashen duniya da su zabi hawa teburin shawara maimakon yin fito na fito, su hade kai maimakon warewa, su kuma rungumi dukkanin hanyoyin hadin kai, su yi watsi da kariyar kasuwa, da danniya ko nuna karfi a siyasance.

Shugaba Xi ya ce tattalin arzikin kasarsa na cikin wani kyakkyawan yanayin ci gaba, inda ma’aunin GDP a bara ya karu da kaso 8 bisa dari, inda kasar ta samu bunkasuwa, da kuma karancin hauhawar farashin hajoji. A hannu guda kuma, kasar ta fuskanci matsi ta fuskar yanayin hada hadar tattalin arzikin kasa da kasa, amma duk da haka, jigon tattalin arzikin kasar, mai kunshe da juriya, da karko da wanzuwar ci gaba mai dorewa har yanzu ba su canza ba.

Har ila yau, shugaban na Sin ya ce, ba burin kasar sa ba ne wanzar da daidaito kadai, domin kuwa a matakin farko akwai bukatar fadada gajiya, sannan a rarraba ta yadda ya kamata, ta hanyar tsarin aikin hukumomi masu ruwa da tsaki. Kamar yadda igiyar ruwa kan shafi daukacin jiragen ruwa, sannu a hankali kowa zai amfana daga ci gaba, kuma alfanun ci gaban zai amfani daukacin mutane, ta hanyoyi mafiya wanzuwa kuma bisa daidaito.

Shugaba Xi ya ce Sin ba za ta cimma burin ci gaba ta hanyar gurgunta albarkatun ta, ko lalata yanayin muhalli ba. Kana ba za ta sadaukar da ci gaba domin kare muhalli kadai ba. Ya kuma kwatanta sadaukar da muhalli domin raya tattalin arziki a matsayin dabara mai kamar "kwashe ruwan cikin gulbi domin kama kifi," yayin da sadaukar da ci gaba domin kare muhalli ke zama tamkar "Hawa bishiya domin kamo kifi".

Xi Jinping ya bayyana kwarin gwiwar sa, game da shirin kasar Sin na gudanar da gasar Olympic da ajin gasar na nakasassu dake tafe a birnin Beijing, cikin kyakkyawan yanayin tsaron lafiya.

Ya ce taken gasar Olympic ta birnin Beijing ta 2022 shi ne, "Aiki tare domin makomar bai daya ga bil adama. Ko shakka babu fatan shi ne a yi hadin kai bisa karfin zuciya, da aiki tare, domin makomar bai daya ta bil adama." (Saminu)