logo

HAUSA

Sin ta aike da ton 4,000 na shinkafa ga Syria a matsayin tallafin jin kai

2022-01-17 11:02:11 CRI

Sin ta aike da ton 4,000 na shinkafa ga Syria a matsayin tallafin jin kai_fororder_220117-Ahmad 2-China Aid to Syria

A jiya Lahadi, kasar Syria ta karbi sama da ton 4,000 na shinkafa daga kasar, wanda shi ne tallafin jinkai na baya bayan nan da kasar Sin ta samar ga kasar Syria domin saukakawa alummar Syrian dake cikin matsanancin hali.

Feng Biao, jakadan kasar Sin a Syria, ya sanya hannu kan takardun karbar tallafin kayan abincin tare da Khaled Hboubati, shugaban hukumar agaji ta Syrian Arab Red Crescent (SARC), a helkwatar hukumar agajin ta SARC dake Damascus, babban birnin kasar.

Yayin da yake sanya hannu kan takardun karbar tallafin kayayyakin abincin, Hboubati ya godewa kasar Sin bisa taimakon da take baiwa al’ummar kasar Syrian.

Jakadan na Sin ya yi fatan taimakon da kasarsa ke ci gaba da bayarwa zai kawar da wahalhalun da alummar Syria ke fuskanta. (Ahmad Fagam)