logo

HAUSA

Jami’an Afirka sun nuna goyon baya kan gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing

2022-01-16 16:35:13 CRI

Jami’an Afirka sun nuna goyon baya kan gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing_fororder_hoto1

A ranar 13 ga wata, shugaban kasar Comoros Azali Assoumani ya bayyana cewa, ko da yake, ana fuskantar matsalar yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19, amma, tabbas ne, kasar Sin za ta cimma nasarar gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta lokacin hunturu, za ta kuma kare tsaro da lafiyar ‘yan wasan kasashen duniya, da ma jama’ar kasar Sin yadda ya kamata. Kasar Sin ta kware wajen gudanar da babbar gasar wasannin motsa jiki, tabbas ne, za ta cimma nasara wajen karbar bakuncin gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing.

Haka kuma, shugaban kwamitin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics na kasar Mali ya bayyana cewa, kasarsa tana goyon bayan kasar Sin wajen gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing ta shekarar 2022, haka kuma, ba ta goyon bayan siyasantar da gasar Olympics.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympics na kasar Namibiya ya ce, “kasancewa tare” wani muhimmin bangare ne cikin taken Olympics, kwamitin gasar Olympics na kasar Namibiya ba zai amince da wadanda ke neman siyasantar da gasar wasannin motsa jikin ba, kuma, yana goyon bayan gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Beijing, da fatan Sin za ta cimma nasarar gudanar da gasar yadda ya kamata. (Maryam)