logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin zai ba da amsa ga tambayoyin da mutanen duniya za su yi game da kasarsa

2022-01-16 16:21:45 CMG

Shugaban kasar Sin zai ba da amsa ga tambayoyin da mutanen duniya za su yi game da kasarsa_fororder_220116-Xi-Bello

A gobe Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taro ta kafar bidiyo na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya na shekarar 2022, inda zai gabatar da jawabi mai muhimmanci.

Yanzu haka duniyar mu na ci gaba da fuskantar sauyawar yanayi da yaduwar cutar COVID-19, abun da ya sa mutanen duniya ke neman tabbatar da wasu dabarun da za a iya dauka don tinkarar kalubalolin. Bisa la’akari da wannan yanayin da ake ciki, jawabin da shugaba Xi zai gabatar yana da muhimmiyar ma’ana.

Hakika shugaban ya riga ya ba da amsa ga tambayar da aka yi masa cewa “Ta yaya za mu iya ci gaba da raya duniyarmu”, yayin da yake gabatar da jawabai a bukukuwa daban daban da ya halarta, inda a wani tunani mai cike da basira da ya gabatar a madadin kasar Sin ya burge mutanen kasashe daban daban.

Sa’an nan wadanne ayyuka ne kasar Sin ta gudanar, musamman ma a fannonin hulda da sauran kasashe, da tabbatar da tsaro, da raya tattalin arziki, da musayar al’adun dan Adam? Bari mu sa lura kan wannan muhimmin jawabi da shugaba Xi Jinping zai gabatar gobe. (Bello Wang)

Bello