logo

HAUSA

Somalia ta yi Allah wadai da harin kunar bakin wake kan kakakin gwamnatin kasar a Mogadishu

2022-01-16 20:55:59 CRI

Somalia ta yi Allah wadai da harin kunar bakin wake kan kakakin gwamnatin kasar a Mogadishu_fororder_somali

Firaministan kasar Somalia Mohamed Roble, a yau Lahadi ya yi Allah wadai da harin kunar bakin waken da aka kaiwa kakakin gwamnatin kasar Mohamed Ibrahim Moalimuu a Mogadishu, babban birnin kasar Somalia, a wannan rana.

Roble ya ce, Moalimuu, wanda tsohon ‘dan jarida ne ya samu raunuka a sanadiyyar harin da aka kai masa da tsakar rana a yankin Dabka, wata mahadar hanya dake birnin Mogadishu, kuma a halin yanzu yana cikin yanayi mai kyau.(Ahmad)