logo

HAUSA

Wakilin Sin: Kasar Sin za ta kiyaye matsayinta na sahihiyar aminiyar sauran kasashe masu tasowa

2022-01-16 16:34:31 CMG

Wakilin Sin: Kasar Sin za ta kiyaye matsayinta na sahihiyar aminiyar sauran kasashe masu tasowa_fororder_220116-kasashe masu tasowa-Bello

Wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya bayyana a ranar Juma’a yayin wani biki na kungiyar G77 cewa, a cikin sabuwar shekarar 2022 da muke ciki, kasar Sin za ta karfafa hadin gwiwarta da mambobin G77, da kokarin kiyaye matsayinta na wata sahihiyar aminiyar sauran kasashe masu tasowa.

A cewar Mista Zhang, duniyarmu na ci gaba da fuskantar wasu matsaloli, musamman ma a fannonin dakile cutar COVID-19, da farfado da tattalin arziki a kasashe daban daban, abun da ya sa ake gamuwa da wahala a kokarin aiwatar da ajandar 2030 ta raya kasashen masu tasowa. Wannan yanayi ya sa hadin gwiwar G77 da kasar Sin na da matukar muhimmanci.

Jami’in ya jaddada bukatar karfafa hadin kai ta fuskar dakile annobar COVID-19, da kokarin raya tattalin arizki. A cewarsa, dole ne a martaba moriyar jama’a, don ta zama a gaban kome, da raba fasahohi na dakile cuta tare da kasashe masu tasowa daban daban, da aiwatar da hadin kai a fannonin samar da alluran rigakafi, da sauran magunguna. Ban da wannan kuma, sai a kara lura da bukatu na kasashe masu tasowa, a bangarorin rage talauci, da tara kudi don gina kasa, da tsaron abinci, da na makamashi, da dai sauransu. (Bello Wang)

Bello