logo

HAUSA

Mutane 13 sun mutu a sakamakon hare-hare da aka kai wa kauyuka biyu dake arewa ta tsakiyar Nijeriya

2022-01-15 16:48:16 CRI

‘Yan sandan Najeriya sun tabbatar a jiya cewa, an kai hare-hare ga kauyuka biyu na jihar Naija dake arewa ta tsakiyar Najeriya a kwanakin baya, wadanda suka haddasa mutuwar mutane 13.

Jami’in hukumar ‘yan sandan jihar Nijer ya bayar da sanarwa a wannan rana cewa, wasu dakaru sun kai hare-hare kan kauyuka biyu dake yankin Shiroro na jihar, wadanda suka harbe manoma da suke yin aiki a gona guda 13 har lahira. Domin kauyukan suna nesa da birane, akwai wahalar  sufuri da sadarwa a yankunan, saidai ‘yan sandan jihar ba su samu labari game da faruwar lamarin akan lokaci ba. A halin yanzu, an riga an tura wasu ‘yan sanda zuwa kauyukan don tabbatar da tsaro da magance sake abkuwar harin.

Gwamnan jihar Naija Abubakar Bello ya bayar da sanarwa a wannan rana, inda ya yi Allah wadai da hare-haren. Ya ce, yanzu yanayin girbin amfanin gona ne, hare-haren suna tsorata manoma, watakila zai kawo illa ga girbin hatsi, hakan zai iya haddasa rashin samun wadatar abinci. (Zainab)