logo

HAUSA

Sin ta shirya tsaf don gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing

2022-01-15 16:46:43 CRI

Sin ta shirya tsaf don gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing_fororder_0115-1

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a jiya cewa, duniya na fatan ganin Sin ta iya gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing yadda ya kamata, kana Sin ta riga ta kammala shiryawa gasar a dukkan fannoni.

A ranar 10 ga wannan wata, tashar yankin arewacin nahiyar Amurka ta babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG ta gudanar da wani bikin yayata gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing a dakin wasannin motsa jiki na Washington dake kasar Amurka, inda mutanen kasar Amurka da dama sun nuna fatan alheri ga gasar. Game da wannan batu, Wang Wenbin ya bayyana cewa, ya kalli bidiyon bikin, mai cike da nau’ikan kayayyakin gargajiyar Sin da na nuna fatan alheri ga gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing, kana mutanen Amurka sun nuna farin cikinsu a wajen bikin. Wannan ya shaida cewa, gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing, gagarumin biki ne ga ‘yan wasa mahalarta gasar da masu sha’awar wasan a duk duniya, kana mutanen kasar Amurka da na sauran kasashe suna zumudin ganin an gudanar da gasar yadda ake bukata.

Wang Wenbin ya jaddada cewa, Sin ta yi imani bisa tunanin Olympics da kuma kokarin da bangarori daban daban suke yi, sa’an nan Sin za ta gudanar da wata gasar wasannin Olympics mai nagarta kuma cikin yanayin tsaro, ta hakan za a kara kawo wa mutanen duniya karfin zuci da imani da kuma hadin gwiwa bisa yanayin tinkarar cutar COVID-19. (Zainab)