logo

HAUSA

MDD ta fidda tambarin “wasanni don zaman lafiya” don murnar wasannin Olympic na lokacin hunturu na 2022

2022-01-15 16:01:31 CMG

MDD ta fidda tambarin “wasanni don zaman lafiya” don murnar wasannin Olympic na lokacin hunturu na 2022_fororder_220115-UN releases-Ahmad

Hukumar kula da aike sakonni ta MDD (UNPA), a ranar Juma’a ta fitar da sabon tambari mai taken “wasanni don tabbatar da zaman lafiya” domin murnar gasar wasannin Olympic na lokacin hunturu na Beijing 2022.

UNPA, ta bayyana a taron manema labarai cewa, wannan shi ne karo na farko a tarihi da hukumar ta gabatar da tambarin a wasannin Olympic na lokacin hunturu.

Wasannin na Olympic na lokacin hunturu karo na 24 za su gudana ne a ranar 4 zuwa 20 ga watan Fabrairu a Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

A watan Disambar shekarar 2021, babban taron MDD ya amince da gasar  wasannin Olympic ta lokacin hunturu ta Beijing 2022 don ta kasance a matsayin wani ruhin zaman lafiya, inda aka bayyana gudunmawar da wasanni ke bayarwa wajen daga matsayin tabbatar da zaman lafiya da hadin kan al’ummun duniya.

Kudirin wanda aka baiwa taken “Gina zaman lafiya da ingantacciyar duniya ta hanyar wasanni, kana wasannin Olympic a matsayin ma’auni" inda aka bukaci kiyaye amfani da gasar wasannin Olympic na lokacin hunturu da ajin gasar ta nakasassu ta Beijing 2022 a matsayin ruhin wanzar da zaman lafiya, daga kwanaki bakwai kafin bude gasar wasannin ta Olympic, a ranar 4 ga watan Fabrairun 2022, har zuwa kwanaki bakwai na bayan kammala wasannin ajin nakasassu.

Wasannin na Olympic sun samar da muhimman damammaki wajen yin amfani da tasirin da wasannin ke da shi don cimma burin samar da kyakkyawan yanayin zaman lafiya, da cigaba, da sauye-sauye, da amincewa da juna, da kuma kara fahimtar juna a tsakanin kasashen duniya.(Ahmad)

Ahmad