logo

HAUSA

Xi ya jaddada muhimmancin kiyaye tsaron kasa da zaman lafiya da kare rayukan al’umma

2022-01-15 16:32:44 CMG

Xi ya jaddada muhimmancin kiyaye tsaron kasa da zaman lafiya da kare rayukan al’umma_fororder_220115-Xi-Ahmad

Babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping, ya bukaci a kara himma don tabbatar da kiyaye tsarin jagorancin kasa, da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da kuma tabbatar da tsaron rayuwar al’ummar kasa.

Xi, wanda shi ne shugaban kasar Sin, kana shugaban hukumar koli ta sojojin kasar, yayi wannan kira ne cikin umarninsa na baya bayan nan ga jagororin hukumar siyasa da na shari’a.

Cikin umarnin da ya bayar, shugaba Xi yace, ya kamata a kara himma wajen tabbatar da ganin an yiwa kowane dan kasa adalci.(Ahmad)

Ahmad