logo

HAUSA

Sin ta yi amfani da karin jarin waje a shekarar 2021

2022-01-14 11:06:05 CRI

Sin ta yi amfani da karin jarin waje a shekarar 2021_fororder_220114-S3-Sin

Sabbin alkaluman da ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, adadin jarin waje da Sin ta yi amfani da shi a shekarar 2021 da ta gabata, ya haura kudin kasar Yuan tiriliyan 1.1, adadin da ya dara wanda kasar ta taba samu a baya, yayin da mizani da ingancin tsarin amfani da jarin wajen na Sin ke kara bunkasa.

A shekarar ta 2021, cikin shekara guda, Sin ta samu karin kaso 14.9 bisa dari na jarin waje da ta yi amfani da shi. Sassan dake kan gaba a wannan fanni su ne na masana’antun manyan fasahohi, da fannin ba da hidima, inda bangaren masana’antun manyan fasahohi ya samu karin kaso 17.1 bisa dari, ciki har da masana’antu samar da hajoji da suka samu karuwar kaso 10.7 bisa dari, yayin da tsagin masana’antun manyan fasahohi na samar da hidima, suka samu karuwar kaso 19.2 bisa dari.

Alkaluman sun nuna yadda amfani da jarin waje a fannin ba da hidima, ya kai darajar kudin Sin biliyan 906.49 cikin shekara guda a shekarar ta bara, karin da ya kai na kaso 16.7 bisa dari. (Saminu)