logo

HAUSA

Jimillar kudaden cinikayyar shige da fice na Sin a bara sun haura dala tiriliyan 6

2022-01-14 11:20:51 CRI

Jimillar kudaden cinikayyar shige da fice na Sin a bara sun haura dala tiriliyan 6_fororder_220114-S4-Sin2-cinikayya

A karon farko, jimillar kudaden cinikayyar shige da fice na Sin sun haura dala tiriliyan 6, a cewar kakakin hukumar kwastam, kuma daraktan kididdiga da nazarin alkaluma na kasar Sin Li Kuiwen. Jimillar kudaden cinikayyar hajojin shige da fice na Sin a shekarar ta bara, ya kai kudin Sin yuan tiriliyan 39.1, wanda ya shaida karuwar kaso 21.4 bisa dari kan na shekarar 2020. Cikin wannan adadi, bangaren hajojin da ake fitarwa na da yuan tiriliyan 21.73, wato karuwar kaso 21.2 bisa dari ke nan, yayin da na hajojin da ake shigowa da su ya kai tiriliyan 17.37, da karuwar kaso 21.5 bisa dari.

Kakakin wanda ya bayyana alkaluman, yayin taron ’yan jaridu da ofishin yada labarai na majalissar gudanarwar kasar Sin ya kira da safiyar Juma’ar nan, ya ce matsayin da Sin ta cimma a wannan fanni, ya karya matsayin bajimtar da ta kafa a karon farko, inda jimillar kudaden cinikayyar shige da ficen ta suka haura dala tiriliyan 6, zuwa dala tiriliyan 6.05.    (Saminu)