logo

HAUSA

Kwamitin binciken hakkin dan adam na MDD ya yi Allah wadai da Amurka kan amfani da Guantanamo

2022-01-14 16:14:33 CRI

Kwamitin binciken hakkin dan adam na MDD ya yi Allah wadai da Amurka kan amfani da Guantanamo_fororder_220114-A4-推送

Kwamitin kwararru mai zaman kansa wanda hukumar kare hakkin bil adama ta MDD ta kafa game da batutuwan dake shafar hakkin dan adam, ya fidda sanarwa inda ya yi Allah wadai da matakin kasar Amurka na ci gaba da amfani da gidan yarin Guantanamo. Inda kwamitin ya bayyana lamarin da cewa, tamkar “yin lahani ne ga doka da oda." Sanarwar ta bayyana cewa, tsare mutanen da ake yi ba bisa ka’ida ba, da gallazawa ko kuma cin zarafin mutanen da Amurka ke aikatawa a gidan yarin Guantanamo a tsawon shekaru 20 ba tare da yi musu shara’a ba babu wata gwamnati a duniya da za ta lamunta. (Ahmad Fagam)