logo

HAUSA

Wakilin Sin a MDD ya yi Allah wadai da masu nuna kiyayya ga Sin inda suke yada karairayi kan yankin Xinjiang

2022-01-13 11:37:33 CRI

Wakilin Sin a MDD ya yi Allah wadai da masu nuna kiyayya ga Sin inda suke yada karairayi kan yankin Xinjiang_fororder_220113-Ahmad4-Xinjiang

Kasar Sin ta bayyana kin amincewarta gami da yin Allah wadai da wani makircin da makiyan kasar Sin suka shirya da suke kira wai “Kotun shara’ar Uyghur", kakakin ofishin wakilcin dindindin na kasar Sin a MDD ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Laraba.

A cewar sanarwar, abin da ake kira wai ‘kotu’ da ‘shara’arsu,’ ba komai ba ne sai makircin siyasa wanda makiyan kasar Sin ke daukar nauyi kuma yunkurin nasu abin kunya ne wanda ya saba doka kuma ya ci karo da gaskiya.

Kakakin ya jaddada cewa, duk wani yunkurin duk wata kasa, kungiya, ko kuma daidaikun mutane, dake neman hargitsa yankin Xinjiang da shafawa kasar Sin kashin kaza ba zai taba samun nasara ba. (Ahmad Fagam)